Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Sama Da Mutane 50 A...

‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Sama Da Mutane 50 A Katsina

128
0

‘Yan bindiga sun sake sace akalla mutane 50 a kauyen Ruwan Godiya da ke karamar hukumar Faskari ta Jihar Katsina.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunan sa ya shaida wa manema labarai cewa, sama da ‘yan bindiga 60 a kan babura ne su ka shiga garin su ka bude wuta.

Ya ce ‘yan bindigar sun kwashe sama da sa’o’i biyu su na cin Karen su babu babbaka, inda su ka kwashe dukiyoyin jama’a ciki har da kayan abinci da tufafi kafin su kora jama’a.

Jihar Katsina dai na ci-gaba da fuskantar munanan hare-haren ‘yan bindiga, wadanda ke hallaka jama’a ba tare da kaukautawa ba.

Leave a Reply