Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Barkewar Sabon Rikici A Jihar Cross River

‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Barkewar Sabon Rikici A Jihar Cross River

96
0

Rahotanni daga jihar Cross Rivers na cewa, an kashe wani Bishop da wani masanin tarihi a wani sabon rikicin kabilanci da ya barke a yankin a karamar hukumar Biase.

Kisan da aka yi dai ya na daga cikin zazzafan rikicin kabilanci tsakanin kabilun Abanwan da Urugbam a cikin kabilar Erei, inda aka kona Bishop da ran sa tare da fille kan dan sa a wani sabon fadan kabilanci da ya shafi al’ummomin biyu.

Wasu majiyoyi daga al’ummar yankin, sun ce an yi wa Limamin Kiristan kwanton bauna ne tare da dan sa, yayin da su ke kan babur daga unguwar Abanwan zuwa Afikpo da ke kusa da jihar Ebonyi.

Al’ummar Erei dai sun shafe tsawon shekaru su na takun-saka a kan wani fili da yankin ya kafa kafin yakin basasar Nijeriya a matsayin matsugunin gonar ‘ya’yan manja.

Yanzu haka dai hukumomin tsaro daga helkwatar rundunar soji ta tabbatar da tura sojoji a yankin Abanwan da Urugbam domin kwantar da tarzomar.

Leave a Reply