Home Labaru ICPC Ta Gano Yadda Aka Sayi Gidaje 301 Da Haramtattun Kudade A...

ICPC Ta Gano Yadda Aka Sayi Gidaje 301 Da Haramtattun Kudade A Abuja

21
0

Hukumar yaki da rashawa ICPC, ta ce ta samo gidaje 301 daga jami’an gwamnati, wadanda aka saye da haramtattun kudade a birnin tarayya Abuja.

Shugaban hukumar Bolaji Owasanoye ya bayyana haka, a wani taron da kwamitin wucin-gadi na majalisar wakilai ya shirya a kan ayyukan masu saida da filaye da gidaje a birnin tarayya.

Owasanoye, ya ce hukumar ICPC ta samu korafe-korafe daban-daban a kan ayyukan handama, ya na mai cewa rashin rijistar gidaje da filaye a birnin tarayya yadda ya dace ne ya janyo rashawa a bangaren.

Mataimakin daraktan hukumar EFCC Daniel Esei, ya ce ya dace a karfafa hukumar, ta yadda za ta rika daukar mataki a kan wadanda ta kama da laifin boye kudaden haram.