Home Labaru Ban Taba Karbo Bashin Ko Sisi Ba Lokacin Ina Gwamna – Kwankwaso

Ban Taba Karbo Bashin Ko Sisi Ba Lokacin Ina Gwamna – Kwankwaso

9
0

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce lokacin da ya ke gwamnan jihar na tsawon shekaru 8 bai taba karbo bashin ko sisin Kobo ba.

Kwankwaso ya bayyana haka ne, yayin tattaunawa da shi a gidan talabijin na Arise, inda ya zargi Gwamna Ganduje da jefa jihar Kano cikin halin ƙaƙani kayin bashi.

Sanata Kwankwaso ya kara da cewa, mafi yawan ayyukan da gwamna Ganduje ke yi da kuɗaɗen bashin ba su zama dole ba.

Ya ce a tafiyar kwankwasiyya ba su yarda da karɓo bashi ba, sai dai idan abin da za a yi ya zama wajibi, ya na mai alfaharin cewa lokacin ya na gwamna bai taba cin bashin ko naira ɗaya ba, maimakon haka ma ya ce sun biya bashin da wasu su ka kinkimo masu ne.