Home Labarai Kotu Ta Umarci INEC Ta Tabbatar Da Akpabio

Kotu Ta Umarci INEC Ta Tabbatar Da Akpabio

343
0

Babbar Kotun Tarayya ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa ta maida sunan Ministan Neja Delta Godswill Akpabio a matsayin dan takarar Sanatan mazabar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma a karkashin Jam’iyyar APC.

Kotun ta bada umarnin ne, bayan hukumar zaben ta cire sunan Akpabio, wanda ya nemi takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC kafin daga baya ya janye a matsayin dan takarar sanata.

A baya dai jam’iyyar APC ta mika wa hukumar zabe sunan Akpabio a matsayin dan takarar Sanatan Akwai Ibom ta Arewa maso Yamma, yayin da ta mika sunan Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan a matsayin dan takarar Yobe ta Arewa.

Haka kuma, jam’iyyar ta gabatar da Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi a matsayin dan takarar Sanatan mazabar Ebonyi ta Kudu, sai dai kuma a jerin sunayen ‘yan takarar da hukumar zabe ta fitar babu sunan ko daya daga cikin su.

Leave a Reply