Akalla shaguna 100 ne su ka kone sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwar Shagamu da ke jihar Ogun.
Gobarar dai ta tashi ne a tsakar dare daga layin masu saida tufafi sannan ta yadu zuwa wasu sassan kasuwar kamar yadda rahotanni su ka ruwaito.
Shugabannin kungiyoyin masu ruwan leda da kayan sha a kasuwar Remo zone da Adetola Soyemi, sun shaida wa manema labarai cewa sama da shaguna 100 ne su ka salwanta a gobarar.
Jami’an biyu, sun yi zargin gobarar ta tashi ne sakamakon matsalar wutar lantarki, sai dai ba za a iya tabbatar da gasikyar hakan ba.
You must log in to post a comment.