Home Labaru Kiwon Lafiya Zazzabin Lassa: Mutum Daya Ya Rasa Ran Sa A Jihar Kaduna

Zazzabin Lassa: Mutum Daya Ya Rasa Ran Sa A Jihar Kaduna

404
0
Zazzabin Lassa: Mutum Daya Ya Rasa Ran Sa A Jihar Kaduna
Zazzabin Lassa: Mutum Daya Ya Rasa Ran Sa A Jihar Kaduna

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kaduna, ta tababtar da mutuwar wani matashi sakamakon kamuwa da zazzabin Lassa.

Kwamishinar lafiya ta jihar Kaduna Amina Baloni, ta ce mutumin ya rasu ne a ranar Lahadin da ta gabata.

Ta ce sakamakon gwajin da aka yi wa mutane 11 da ake zargin su na dauke da kwayar cutar, ya nuna cewa bakwai daga cikin su ba su dauke da ita.

Mutum 38 da ake zargi su na dauke da kwayar cutar kuma na samun kulawa, yayin da ake kokarin dakile yaduwar ta.

Kwamishinar, ta kuma karyata jita-jitar rufe asibitin koyarwa na Barau Dikko domin killace masu dauke da kwayar cutar, inda ta ce asibitin ya dauki matakan takaita ziyartar majinyata ne domin kawar da kamuwa da wasu cututtuka masu yaduwa baya ga zazzabin Lassa.