Home Labaru IBB Ya Bayyana Nijeriya A Matsayin Kasa Mai Sarkakiya

IBB Ya Bayyana Nijeriya A Matsayin Kasa Mai Sarkakiya

900
0
Ibrahim Badamasi Babangida, Tsohon Shugaban Kasa
Ibrahim Badamasi Babangida, Tsohon Shugaban Kasa

Tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce mulkin Nijeriya akwai wahala, ya na mai bayyana ta a matsayin kasa mai sarkakiya da wahalar tafiyarwa saboda yanayin al’ummar ta da bambance-bambancen su.

Janar Babangida ya ce, bambance-bambance sun kawo ra’ayoyi mabambamta tare da zafafan muhawurori,wadda wani lokaci ke kaiwa ga kiyayya ko tashin hankali.

Da ya ke jawabi yayin ziyarar da wasu shugabannin marasa rinjaye na majalisar wakilai a karkashin jagorancin Ndudi Elumelu su ka kai a gidan sa da ke Minna, Babangida ya bayyana Nijeriya a matsayin kasa mai karsashi da ban sha’awa. IBB, ya kuma bukaci ‘yan siyasa kada su karaya da sarkakiyar Nijeriya, maimakon haka, ya ce su maida hankali wajen ciyar da ita gaba ta fuskar amfani da yanayin al’ummar ta.