Home Labaru DPR Ta Garkame Gidajen Man Fetur 53 A Jihar Kaduna

DPR Ta Garkame Gidajen Man Fetur 53 A Jihar Kaduna

314
0
Hukumar Kula Da Saida Man Fetur Ta Kasa, DPR
Hukumar Kula Da Saida Man Fetur Ta Kasa, DPR

Hukumar Kula da Saida Man Fetur ta Kasa DPR shiyyar Kaduna, ta kulle gidajen saida man fetur da iskar gas guda 56 a fadin jihar Kaduna.

DPR ta bayyana cewa, ta kulle gidajen man ne saboda sun ki bin ka’idojin da su ka jibinci saida man fetur da iskar gas a fadin duniya.

Babban Jami’in hukumar mai kula da Shiyyar Kaduna Isa Tafida ya bayyana haka, yayin da ya ke zagayen gani-da-ido  a gidajen mai na watan Yuli a jihar Kaduna.

Ya ce sun gudanar da samamen kulle gidajen man ne, domin zakulo masu boye mai da masu karkatar da shi da kuma masu saidawa sama da farashin da aka kayyade a kowace lita.

Isa Tafida ya kara da cewa, sun kulle wasu gidajen mai saboda ba su saida shi gaba daya a gidan mai, yayin da wasu ke gudanar da harkar mai ba tare da lasisi ba, ko kuma wadanda lasisin su ya kare amma sun ki zuwa a sabunta masu.

Ya ce sauran kuma sun kama su ne su na saida mai a wuraren da babu matakan tsaron lafiya, ko kuma rashin cika sharuddan bin dokokin kare hadurra ko rashin kula da muhimmancin rayuwar jama’a da dukiyoyin su.