Home Labaru HURIWA Ta Bukaci Buhari Ya Fatattaki Lai Mohammed

HURIWA Ta Bukaci Buhari Ya Fatattaki Lai Mohammed

57
0

Kungiyar marubuta masu kare hakkin dan Adam a Nijeriya, HURIWA, ta bukaci a kori ministan yada labarai da al’adu Lai Mohammed, a kuma kama shi tare da gurfanar da shi, bisa zargin shi da karya game da abin da ya faru a Lekki tollgate da ke jihar Legas a shekarar da ta gabata.

HURIWA ta yi ikirarin cewa, ministan bai fadi gaskiyar abin da ya wakana ba, lamarin da janyo sabani a bangaren kwamitin bincike na Legas.

Wannan dai, ya na kunshe ne a cikin wata takarda bayan bayyana sakamakon binciken kwamitin jihar Legas na bin diddigin lamarin da ya faru a Lekki.

Ta ce duk da Ministan ya yi ikirarin cewa babu wanda aka kashe, amma kwamitin ya ce tabbas an kashe mutane masu tarin yawa.

Rahoton kwamitin dai ya bayyana yadda aka rika harbe-harbe da kuma cin zarafin jama’a da ‘yan sanda su ka yi, tare da take hakkin bil adama da jami’an tsaro su ka aikata.