Home Labaru ‘Yan A-waren Kamaru Sun Kashe Mutane A Jihar Taraba

‘Yan A-waren Kamaru Sun Kashe Mutane A Jihar Taraba

88
0

Wasu da ake zargin ‘yan awaren Ambazonia ne daga kasar Kamaru, sun tafka barna a karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.

Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa Sanata Emmanuel Bwacha, ya ce wadanda ake zargin sun bindige hakimin kauyen da wasu mazauna unguwar Manga.

Yayin da ya ke tabbatar da lamarin a zauren majalisar dattawa,

Sanatan ya ce an kashe mutanen ne yayin farmakin da ‘yan awaren Kamaru su ka kai yankin.

Sanatan Bwacha, ya ce mamayar ‘yan A-Waren na iya zama barazana ga yankunan Nijeriya, dominhar yanzu ba a san dalilin shigowar su ba, don haka ya yi kira ga sojoji su gaggauta daukar mataki domin dakile mamayar da ‘yan A-Waren ke yi.