Home Labaru Hukunci: Jamhuriyyar Benin Ta Tsawaita Wa’adin Tsare Sunday Igboho Da Wata Shida

Hukunci: Jamhuriyyar Benin Ta Tsawaita Wa’adin Tsare Sunday Igboho Da Wata Shida

62
0

Gwamnatin Jamhuriyyar Benin ta tsawaita wa’adin tsare mutumin nan mai rajin kare hakkin Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho da watanni shida a Cotonou, babban birnin kasar.

Wannan dai na cin karo da sanarwar da wani lauya mai kare hakkin bil Adama da ke Abuja, Pelumi Olajegbesi ya yi a karshen makon da ya gabata cewa za a saki Igboho nan ba da jimawa ba.

Sai dai da yake martani kan sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi, lauyan Igboho, Yomi Aliyu ya ce gwamnatin Jamhuriyyar Benin ta sabunta wa’adin tsare wanda yake wakilta ne na tsawon watanni shida duk da cewa ba a tuhumarsa da aikata wani babban laifi kuma babu wata bukata da aka shigar ta taso keyarsa zuwa Najeriya daga gwamnatin kasar.

Wasu majiyoyi sun ruwaito cewa, tun a watan Yulin 2021 ne Sunday Igboho ya shiga hannu bayan jami’an tsaron kasar da ke yankin Yammacin Afirka suka yi ram da shi a filin jirgin saman Cotonou yana kokarin guduwa Jamus.

Bayanai sun ce wata kotu ce dai a Benin ta bayar da umarnin a kai jagoran masu fafutikar kafa kasar Yarbawa a Najeriya gidan yari da a yanzu ya shafe fiye da kwanaki 200 a tsare bayan ’yan sandan kasar sun cika hannunsu da shi.