Home Home Ta Maula: ‘Yan Senegal Na Bikin Nasarar Kungiyar Kwallon Kafa Ta Les...

Ta Maula: ‘Yan Senegal Na Bikin Nasarar Kungiyar Kwallon Kafa Ta Les Lions De La Téranga

92
0

Al’ummar Senegal sun cika titunan babban birnin kasar Dakar, suna rawa da waka domin yiwa ‘yan wasan kasar maraba lale, bayan yin nasarar cin kofin kwallon kafar Afirka a karon farko da suka yi a ranar Lahadi.

Shugaba Macky Sall ya tarbesu cikin farin ciki da annushawa, ya kuma yi jawabin godiya ga ‘yan wasan da suka fito da kima da martabar kasar.

Mista Sall ya jinjinawa mai horas da ‘yan wasan Aloiu El-Tactico inda yake cewa yana godiya ga Kocin, kamar yadda ake fada bai cika magana ba, baya hayaniya, amma ya na da kwakwalwa, ya kuma jagoranci ‘yan wasan kasar da suka kawo wannan abin alfahari ga kasar tasu.