Home Home Lafiya: Cutar Tamowa Na Barazana Ga Mutum Miliyan 13 A Gabashin Afirka

Lafiya: Cutar Tamowa Na Barazana Ga Mutum Miliyan 13 A Gabashin Afirka

95
0

Akalla mutum miliyan 13 na fuskantar barazanar kamuwa da cutar tamowa a kasashen Somaliya da Habasha da kuma Kenya a cikin ’yan watanni masu zuwa.

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce barazanar ta karu ne a sakamakon kimanin shekara goma da aka kwashe ana fama da tsananin fari a Gashin Afirka.

Wata sanarwa da jami’in hukumar na yankin, Michael Dunford, ya fitar ya bayyana cewa amfanin gona da dabbobi suna mutuwa, yunwa sai karuwa take yi saboda karancin ruwan sama a Gabashin Afirka.

Shekara uku ke nan a jere da ake fama da karancin ruwan sama a kasashen uku, kuma rabon da a samu karancin ruwan sama haka tun a shekarar 1981.

A halin yanzu dai ana rabon kayan abinci a wasu yankunan kasashen Kenya, Habasha da Somaliya inda mutum miliyan 13 ke fama da cutar tamowa.

Akwai hasashen cewa matsananciyar yunwa za ta addabi yankin a cikin watanni ukun farkon shekarar da muke ciki ta 2022.