Ministan Sadarwa Ali Isa Pantami, ya yi magana a karon farko bayan Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa ta kira matsayin Farfesan da Jami’ar Fasaha ta Owerri ta ba shi a matsyain haramtacce ne.
Pantami ya yi magana ne yayin da ya ke zantawa da manema
labarai, jim kadan bayan kammala Taron Majalisar Zartarwa a
Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ya ce ba zai ce komai
ba domin taƙaddamar lamarin ta na kotu.
Ya ce a matsayin shi na jami’in gwamnati, ya san laifin shiga
hurumin kotu idan ba ta yanke hukunci a kan shari’a ba, don
haka ba zai ce uffan a kan lamarin ba, domin shi ɗan Nijeriya ne
mai bin doka da oda.
You must log in to post a comment.