Home Labaru Bashin Naira Tiriliyan 25.7 Ake Bin Nijeriya – DMO

Bashin Naira Tiriliyan 25.7 Ake Bin Nijeriya – DMO

180
0

Hukumar Kula da Basussukan da ake bin gwamnatocin Tarayya da Jihohi DMO, ta tabbatar da cewa ana bin Nijeriya bashin naira tiriliyan 25 da biliyan 7.

Babbar Daraktar hukumar Patience Oniha ta bayyana haka, yayin da ta ke jawabi a gaban Kwamitin Kula da Yadda Gwamnati Ke Kashe Kudade na Majalisar Wakilai.

Ta ce ya zuwa watan Yuni na shekara ta 2019 naira tiriliyan 25 da biliyan 7 ake bin Nijeriya bashi, wadanda su ka hada da na tarayya da jihohi da Birnin Tarayya, Abuja.

Patience Oniha, ta ce su na kiran wannan da suna bashin bai-daya, kuma gwamnatin tarayya ce ta ciwo kashi 80 cikin 100 na kudin.

Ta ce kashi 32 cikin 100 na basussukan duk a waje aka ciwo su, yayin da sauran kashi 68 kuma an ciwo su ne a nan cikin gida.