Home Labaru Kiwon Lafiya Hukumar NAFDAC Ta Gargaɗi Mutane Su Daina Cin Ganda

Hukumar NAFDAC Ta Gargaɗi Mutane Su Daina Cin Ganda

766
0
NAFDAC
NAFDAC

Shugaban hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kasa NAFDAC, Moji Adeyeye, ta gargaddi mutane su nesanta kan su daga cin Kirgin dabbobi da aka fi sani da Ganda.

Karanat Wannan: Nukiliyar Iran: An Fara Gudanar Da Wani Taro A Vienna

Adeyeye ta yigargaɗin ne a cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a Abuja.

Ta ce gargaɗin ya zama dole, ganin cewa wasu bara-gurbin ‘yan kasuwa su na saida wa mutane fatar dabbobin da aka Jeme domin maida su takalma ko jaka da sauran su.

Adeyeye, ta ce fatar dabbobin da aka Jeme irin haka ta na cutar da lafiyar mutum, saboda an zuba mata sinadarorin da ke hana su lalacewa.

Ta ce a kan kamu da cututtukan da su ka haɗa da ciwon daji, da ciwon ƙoda da ciwon hanta, da cututtukan da ke kama zuciya da sauran su idan har mutum ya ci irin waɗannan fatu.

A karshe ta ce bisa ga rahotannin wani bincike da su ka gudanar, an shigo da fatun ne daga kasashen Lebanon da Turkey.