Home Labaru ‘Yan Boko Haram Su Kashe Masu Jana’iza 23 A Jihar Borno

‘Yan Boko Haram Su Kashe Masu Jana’iza 23 A Jihar Borno

478
0

Bayanai sun nuna cewa, wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun afka ma wasu mutane da ke kan hanyar su ta dawowa daga makabarta a yankin Nganzai da ke gefen birnin Maiduguri.

‘Yan ta’addan dai sun bude wa mutanen wuta ne, yayin da su ke dawowa daga garin Badu Kuluwa da ke kusa da Goni Abachari su ka kashe mutane 23

Rahotanni sun ce ‘yan sintiri ne su ka kwashe gawarwakin mamatan bayan wadanda su ka samu tsira sun sanar da su.

Maharan Boko Haram dai na yawan kai hare-hare a yankin Nganzai, inda ko a watan Satumbar da ya gabata sun yi sanadiyyar mutuwar mutane takwas a yankin.