Jam’iyyar APC ta soki Farfesa Itse Sagay, saboda ya nuna mamakin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi Sanata God’swill Akpabio a cikin sabbin ministocin sa.
karanta Wannan;
Sagay, wanda Farfesa ne a fannin shari’a kuma baban lauya, ya nuna matukar mamakin yadda shugaba Buhari ya zabi Akpabio a matsayin minista.
Hukumar EFCC dai ta zargi Akpabio da wawurar naira biliyan 108 a lokacin da ya ke gwamna tsakanin shekara ta 2007 zuwa 2015, sai dai an daina jin yadda binciken sa ya kasance, tun bayan da ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma APC a shekara ta 2018.
Sagay ya yi magana a kan sa, inda ya bayyana mamakin sa da cewa, duk cikin sabbin ministocin da shugaba Buhari ya bada sunayen su Akpabio ne kadai ya ke mamaki a kan sa.
Ya ce duk wanda ake zargi da karkatar da kudade bai kamata a nada shi minista ba, amma har yau bai san dalilin da ya sa Shugaba Buhari ya sa sunan shi a cikin sabbin ministocin ba.