Home Labaru Hukumar Kula Da Gidajen Yari Ta Zama Hukumar Gyara Halayya

Hukumar Kula Da Gidajen Yari Ta Zama Hukumar Gyara Halayya

227
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauya sunan hukumar kula da gidajen yarin Najeriya zuwa hukumar gyaran halayya na Najeriya.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, ya ce Buhari ya sauya wannan suna ne bayan rattaba hannu kan wata sabuwar doka da ta raba hukumar zuwa bangare biyu, wadanda suka hada da bangaren dake kula da kulle masu laifi, da kuma bangaren da zai gudanar da ayyukan da ba su shafi kama masu laifi ba.

An kuma kafa sabuwar doka da za ta ba shugaban hukumar na jiha damar kin karbar masu laifi a gidajen gyaran halayya idan har sun cika, domin magance matsalar cunkoson gidajen yari.

Dokar ta ba Alkalin-Alkalai damar mayar da hukuncin kisan daya dauki tsawon shekara 10 ba’a aiwatar dashi ba zuwa hukuncin daurin rai da rai.