Home Labaru Sauke Nauyi: Ahmad Lawal Ya Tabbatar Da Kudirin Majalisar Sa

Sauke Nauyi: Ahmad Lawal Ya Tabbatar Da Kudirin Majalisar Sa

647
0
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa

Bayan kaddamar da sabbin kwamitoci da aka gudanar a baya-bayan nan, shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya ce majalisun dokoki sun shirya tsaf domin sauke nauyin da rataya a wuyar su wajen yiwa ‘yan Najeriya aiki tukuru.

Shugaban majalisar, ya bayyana hakan ne ga manema labarai a harabar babbar tashar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja, jim kadan da dawowar sa daga kasar Saudiyya inda ya gudanar da aikin hajji a bana.

Sanata Lawan ya samu tarba ne daga wasu daga cikin sanatoci da suka hada da Sanata Jibrin Barau, da Sanata Michael Opeyemi Bamidele da kuma shugaban ma’aikatan sa Muhammad Karage. Da yake rokon Allah ya jibinci lamarin Najeriya wajen kawar da duk wani kalubale da take fuskan ta musamman na rashin tsaro, shugaban majalisar ya kuma yiwa Allah godiya da ya bashi damar kasancewa cikin ‘yan Najeriya fiye da dubu 60 da suka sauke farali yayin aikin hajjin na bana.