Home Labaru Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Sabbin Hanyoyi A Katsina

Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Sabbin Hanyoyi A Katsina

422
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu sabbin hanyoyi biyu a yankin Daura dake jihar Katsina.

Buhari ya kaddamar da hanyoyin ne da suka tashi daga Fago zuwa Katsayal da Kwasarawa da Jirdede da Koza, dukkanin su kuma cikin masarautar Daura.

A yayin da yake kaddamar da hanyar  shugaban kasa Buhari, ya ga jami’an Sojojin dake bashi tsaro sanye da rigar kare ruwa, yayin da jami’an ‘yan sandan basu sanye da rigar nan take ya tambayi babban jami’in Dansandan dake cikin tawagar sa dalilin haka.

Shugaba Buhari, ya yi alkawarin tunkarar sufeta janar na ‘yan sanadan Muhammad Adamu, a kan rashin kyautata wa jami’an ‘yan sanda.  Kan batun wutar lanbtarki kuwa, shugaban kasa Buhari ya duba yiwuwar sake kwato kamfanin wutar lantarki na Najeriya, wato NEPA daga hannun ‘yan kasuwa don ceto Najeriya daga matsanancin matsalar wuta da take fama da shi.