Home Labaru Hukumar Kasafta Kudaden Haraji Ta Fara Shirin Sake Tsarin Rabon Kuɗi

Hukumar Kasafta Kudaden Haraji Ta Fara Shirin Sake Tsarin Rabon Kuɗi

6
0
FIRS-Office

Hukumar kasafta Kuɗaɗen haraji ta Ƙasa ta fara shirin sake fasalin rabon kuɗaɗen gwamnati ga tarayya da jihohi da ƙananan hukumomi.

Wata majiya ta ce, za a fara shirin ne ta hanyar gabatar da taron jin ra’ayoyin jama’a kai-tsaye a Legas.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce taron jin ra’ayoyin jama’a da za a fara na yankin Kudu maso Gabas a Legas, zai kasance wanda zai buɗe ƙofar fito da sabon tsarin raba kuɗaɗe a Nijeriya.

Jihohin da za su gabatar da jawabai a wajen taron sun haɗa da Legas da Ekiti da Oyo da Ogun da Osun da kuma Ondo.

A ƙarƙashin tsarin raba kuɗaɗen da ake a kai dai, gwamnatin tarayya ce ke kwasar kashi 52.68 cikin 100 na kuɗaɗen shigar da ake tarawa duk wata, myayin da ake ba jihohi kashi 26.72, ƙananan hukumomi kuma na samun kashi 20.60.