Home Labaru Ma’Aikatar Tsaro Ta Bayyana Wanda Aka Gani Da Bindiga Samfurin Ak-47

Ma’Aikatar Tsaro Ta Bayyana Wanda Aka Gani Da Bindiga Samfurin Ak-47

6
0
The man with gun is not a defense minister

Ma’aikatar tsaro ta musanta rahotannin da ke cewa mutumin da ke dauke da bindiga samfurin AK47 a wani bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumunta ministan tsaro Bashir Magashi ne.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa ministan ta fuskar yada labarai Mohammad Abdulkadir ya fitar, ya ce mutumin da aka gani a cikin bidiyon shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Muhalli ta Sojin Nijeriya  ne da ke Makurdi.

Mohammad Abdulkadir, ya ce duba da yanayin aikin sa, shugaban Kwalejin ya na da ikon doka na daukar makami.

Ya ce ministan tsaro kamar takwarorin sa na sauran ma’aikatu, ya na amfani da bakar mota kirar Land Cruiser jeep ne ba mai launin kore irin ta sojoji ba.