Home Labaru Yadda Malaman Makaranta A Jihar Taraba Ke Rayuwa Watanni Shida Ba Albashi

Yadda Malaman Makaranta A Jihar Taraba Ke Rayuwa Watanni Shida Ba Albashi

6
0
Taraba Primary School Teachers

Malaman makarantun firamare da ma’aikatan kananan hukumomi a jihar Taraba, su na ci-gaba da kuka a kan rashin biyan albashi na tsawon watanni shida.

Wannan dai ya na zuwa ne, yayin da tsadar rayuwa ke kara tsananta sakamakon hauhawar farashin kayan masarufi bayan karuwar farashin dala a Nijeriya.

Ma’aikatan dai su na cewa, sai sun sha baƙar wuya su ke iya riƙe kan su a halin da ake ciki sakamakon rashin biyan su haƙƙokin su.

Daya daga cikin dubban ma’aikatan ya ce, sai an yi kamar za a magance masu matsalar daga baya hannun agogo ya koma baya.

Wata malama da aka zanta da ita cewa ta yi, yanzu ko neman aure malami ya je ba ya samun mai auren shi  sai dai ya nemi bazawara, domin sai ta rika ganin ba zai iya ciyar da it aba.