Home Labaru Horo: An Kori Sojojin Da Aka Kama Su Na Garkuwa Da Kuma...

Horo: An Kori Sojojin Da Aka Kama Su Na Garkuwa Da Kuma Fashi Da Makami

261
0

Hukumar Tsaro ta dakarun Soji, ta bayyana korar wasu sojoji uku da aka kama cikin gungun masu garkuwa da mutane a bayan garin Maiduguri.

Kwamandan Tsara Dabarun Yaki na rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ Olusegun Adeniyi bayyana haka, yayin da ya ke damka korarrun sojojin uku a hannun hukumar ‘yan sanda a Maiduguri.

Manjo Janar Adeniyi, ya ce an kama sojojin tare da wasu mutane 22 da ake zargi da sassafe, a cikin wani gini da ke bayan garin Maiduguri.

Ya ce sojojin da aka kora, an tura su aiki ne a karkashin rundunar ‘Operation Lafiya Dole’, amma su ka bijire su na zuwa yin garkuwa da mutane da fashi da makami da kisa da kuma kungiyar asiri. Adeniyi, ya ce ba su da lokacin ci-gaba da aiki tare da irin wadannan bara-gurbin jami’ai, don haka an kore su kamar yadda ka’idar dokar aikin soji ta tanada.