Home Labaru Tonon Asiri: An Gano Gawar Kwamandar Sojin Ruwan Da Ta Bace Cikin...

Tonon Asiri: An Gano Gawar Kwamandar Sojin Ruwan Da Ta Bace Cikin Rijiya

243
0

Rahotanni na cewa, an tsinci gawar Kwamandar Sojin Ruwa da ta bace cikin makonni biyu da su ka gabata a Kaduna.

An dai gano gawar O.O Ogundana ne a cikin wata rijiya marar zurfi, kamar yadda majiyar sojoji ta shaida wa manema labarai.

Ogundana, ita ce Shugabar Kwalejin ‘ya’yan Sojoji da ke Jaji a jihar Kaduna kafin bacewar ta.

Ana dai yi zargin cewa, wani malamain makarantar da ta ke shugabanta mai suna Simon Bernard ne ya kashe ta. Yayin da ya amsa laifin da ake zargin sa da aikatawa, Simon Bernard ya ce ya aikata haka ne saboda ta cire shi daga shugabancin Kungiyar Iyaye Da Malaman Makaranta, sannan akwai haushin ta yi ma shi alkawarin ba shi naira miliyan 2 da rabi amma ta kasa cikawa.