Home Labaru ‘Yancin Kai: Atiku Abubakar Ya Yi Korafi A Kan Halin Da Nijeriya...

‘Yancin Kai: Atiku Abubakar Ya Yi Korafi A Kan Halin Da Nijeriya Ke Ciki

223
0
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa , Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar, PDP
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa , Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar, PDP

A cikin sakon san a cikar Nijeriya shekaru 59 da sumun ‘yancin kai, dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya yi korafi a kan halin da kasar nan ke ciki.

A cewar sa, magabatan Nijeriya ba za su taba tunanin cewa bayan shekaru 59 da samun yancin kai Nijeriya za ta tsinci kan ta a cikin hali na rashin yancin Jarida da matasa ba, sannan masu rajjin kare hakkin dan Adam su na fuskantar barazanar kamu.

Atiku Abubakar, ya bukaci ‘yan Nijeriya su dauki matakin damokradiyya, domin tabbatar da cewa ba a yi watsi da kudirin magabata na kawo hadin kai da zaman lafiya da ci-gaba ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya kuma bukaci al’ummar Nijeriya su hada kai tare da jajircewa domin inganta al’amurran kasar nan.