Home Labaru Tattalin Arziki: Nnpc Ta Samu Ribar Naira Biliya 287 – Mele...

Tattalin Arziki: Nnpc Ta Samu Ribar Naira Biliya 287 – Mele Kyari

36
0
Mele Kyari

Kamfanin mai na kasa, NNPC ya samu ribar farko a tarihi cikin shekaru 44, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta shaida.

Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ne babban ministan harkokin fetur, ya ce wannan wani ɓangare ne a kokarin su na dabarun tattalin arziki.

Inda ya bayyana cewa a shekara ta 2020 kamfanin na NNPC ya ci ribar dala miliyan 700, wanda hakan gagarumar asara ce.

Har yanzu dai babu cikakun bayanai kan yadda NNPC ya samu irin wannan riba a lokacin da tattalin arzikin kamfanin ke taggayara saboda sauyin farashi a kasuwar duniya da annobar korona ta haifar.

Sanarwar shugaba Buhari na zuwa ne adaidai lokacin da gwamnatinsa ke kokarin rusa NNPC domin bai wa yan kasuwa damar shiga harkar da nufin samar da haɓɓaka.