Home Labaru Harin Kakangi: Jami’an Yan Sanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3 Yankin Birnin...

Harin Kakangi: Jami’an Yan Sanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3 Yankin Birnin Gwari

162
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna, ta sanar da cewa jami’an ta sun hallaka wasu ‘yan bindiga uku da su ka kai hari a kauyen Kakangi da ke karamar hukumar birnin gwari ranar Asabar da ta gabata.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar kaduna Yakubu Sabo, ya ce an yi rashin wasu hafsoshi biyu sakamakon artabu da aka yi tsakanin ‘yan bindigar da jami’an yan sanda.

Idan dai za a iya tunawa, ‘yan bindigar sun afka wa mazauna garin ne yayin da ake gudanar da wani bikin daurin aure.

Jami’an ‘yan sandan da su ka rasa rayukan su kuwa sun hada da Sufeto Aliyu Muhammad, da Sajen Rabi’u Abubakar, dukkan su daga ofishin hukumar da ke Randagi kamar yadda Yakubu Sabo ya bayyana.