Kididdigar cibiyar kula da basussuka ta Nijeriya DMO, ta bayyana cewa jihohin Kaduna da Legas da Cross River da kuma Edo, sun sha gaban sauran jihohin Nijeriya wajen dora mata kantar bashi da su ka ciyo a kasashen ketare.
Binciken da cibiyar ta gudanar ya tabbatar da cewa, jerin jihohin hudu sun ciyo bashi na kimanin dala biliyan 2 da miliyan 12, daga cikin dala biliyan 4 da miliyan 23 da dukkan jihohin Nijeriya 36 da birnin tarayya su ka karbo a kasashen ketare.
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, jihohin 4 kacal sun karbi bashi na sama da rabin kaso na bashin da kasashen duniya ke bibiyar gwamnatin Nijeriya.
Jihohin Legas da Cross River da Edo da Kaduna, sun karbi bashi na sama da kaso 50 cikin 100 na basussukan da ke kan Nijeriya a halin yanzu.
A bashin cikin gida ma jihar Legas ta sake cirar tuta, inda nauyin bashin da ke kan ta ya kai kimanin Naira biliyan 530 da miliyan 24, yayin da jihar Delta ke biye da ita da da bashin Naira biliyan 228 da miliyan 81, sai kuma jihar Ribas mai Naira biliyan 225 da miliyan 59.