Home Labaru Hajjin Bana: Bankin Musulunci Na Duniya Ya Ba Nijeriya Tallafin Naira 186,000,000

Hajjin Bana: Bankin Musulunci Na Duniya Ya Ba Nijeriya Tallafin Naira 186,000,000

496
0

Gwamnatin tarayya ta rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar samun tallafin dala dubu dari biyar da ashirin da uku da dari takwas da ashirin da uku, kimanin naira miliyan dari da tamanin da shida kenan daga babban bankin Musulunci na Duniya.

Wata majiya ta ce an kulla yarjejeniyar ne a birnin Marrakesh na kasar Morocco, yayin taron babban bankin karo na 44, inda ministar kudi Zainab Ahmed ta sanya hannu a madadin Nijeriya, yayin da shugaban bankin Bandar Hajjar ya sa hannu a madadin Bankin.

Zainab Ahmed, ta ce za ayi amfani da kudaden ne wajen horar da jami’an hukumar kula da aikin Hajji ta Nijeriya, tare da sayen duk wasu kayan aiki da hukumar ke bukata da kuma gyaran wasu kayan aikin.

Ta ce gwamnatin Nijeriya za ta yi amfani da wani kaso na kudin wajen gudanar da aikin habbaka sha’anin kamfanonin sarrafa auduga wajen hada kayan sawa a Najeriya, ta hannun ma’aikatar ciniki, kasuwanci da zuba jari.

Da ta ke bayyana yadda za a raba kudaden, Ministar ta ce hukumar kula da aikin Hajji ta kasa za ta samu dala dubu 243,823, yayin da ma’aikatar ciniki za ta samu dala dubu 280,000.