Home Labarai Kudin Fansa: Sojoji Sun Gano Naira Miliyan 60 Da za a Kai...

Kudin Fansa: Sojoji Sun Gano Naira Miliyan 60 Da za a Kai Wa ‘Yan Bindiga

49
0

Rundunar sojin Nijeriya, ta ce dakarun ta sun gano naira miliyan 60 da aka yi nufin kai wa ‘yan ta’adda domin karbo wasu daga cikin wadanda ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su.

Wata majiya ta ruwaito cewa, dakarun sun yi nasarar kubutar da
wasu mutane da aka yi garkuwa da su da su ka hada da mata da
kananan yara.

Dakarun, wadanda su ka hada da sojin sama da na kasa, sun kai
ga cin karfin ‘yan bindigar, inda aka gano muggan makamai da
bindiga kirar AK47 da albarusai da sauran su.

Sojojin sun ce, za su mika batun jami’an tsaron da ake zargi da
kai kudin fansar ga ma’aikatar tsaron Nijeriya domin gudanar da
bincike.