Home Labaru Harin Bam: Mutum Bakwai Sun Mutu A Afghanistan

Harin Bam: Mutum Bakwai Sun Mutu A Afghanistan

309
0

Hukumomi a Afghanistan sun ce wani bam da ya tashi kan hanya a lardin Ghazni  ya kashe mutum bakwai.

Sun ce mata uku da yara biyu da maza biyu ne harin ya rutsa da su yayin da motar da suke ciki ta taka bam ɗin.

Farar hula ne akasari ke shan wuya a rikicin da aka shafe sama da shekaru 40 ana yi a kasar.

Tattaunawa tsakanin gwamnatin kasar da ‘yan kungiyar Taliban na samun tsaiko sakamakon musayar fursunonin da ake yi tsakanin ɓangarorin biyu.

Musayar fursunonin dai na ɗaya daga cikin yarjejeniyar da Taliban ɗin ta yi da Amurka domin a tattauna da Afghanistan sai dai har yanzun ana samun tsaiko.