Home Labaru Zaben 2015: Babacir Ya Ce Tinubu Ne Ya Tarawa Shugaba Buhari Kudin...

Zaben 2015: Babacir Ya Ce Tinubu Ne Ya Tarawa Shugaba Buhari Kudin Kamfe

383
0

Tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya Babacir David Lawal, ya ce Bola Ahmed Tinubu ne ya taka gagarumar rawa wajen tarawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kudin yakin neman zaben da ya taimaka masa samun nasarar zaben shekarar 2015.

A wata hirar da yayi da Jaridar Punch, Babacir yace shugaba Buhari, da magoya bayan sa basu da kudin da zasu iya lashe zabe, sai dai manufofi da kuma goyan bayan da suke da ita a wajen wasu ‘yan Najeriya.

Tsohon Sakataren gwamnatin ya ce Tinubu, ne yayi amfani da ‘yan kasuwar da ya sani wajen tara makudan kudaden da  shugaba Buhari, yayi amfani da su wajen kada Goodluck Jonathan.

Babacir, ya ce daga cikin wadanda suka bada gudummawa harda wasu dake kusa da gwamnatin Jonathan, saboda yadda suka gamsu da tabbacin da Tinubu ya basu.

Tsohon Sakataren gwamnatin yace shi da ministan man fetur Timipre Sylva, sun yi iya bakin kokarin su wajen ganin sun samawa Shugaba Buhari, kudaden yakin neman zabe amma sai suka gaza, har saida Tinubu, ya sa hannu.

Babacir, yace bayan kudaden tallafi da Tinubu ya samawa Buhari, yayi kuma yi amfani da dukiyar sa wajen yakin neman zaben da kuma dauko hayar wadanda suka taimakawa tsohon shugaban Amurka Barack Obama, yakin neman zabe wajen tallata shugaba Muhammadu Buhari.

Leave a Reply