Home Labaru Rikicin PDP: Uche Secondus Ya Janye Daga Taron Kwamatin Zartarwa

Rikicin PDP: Uche Secondus Ya Janye Daga Taron Kwamatin Zartarwa

51
0
Shugaban Jamiyyar PDF - Secondus

Shugaban babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP, Uche Secondus, ya janye daga taron Kwamatin Zartarwa na jam’iyyar da ke gudana yanzu haka.

Rahotanni sun ce akwai yiwuwar Uche Secondus, ya bi umarnin wata kotun Jihar Rivers ce da ta kore shi a matsayin shugaba, inda ya nemi mataimakin sa ya jagoranci taron.

Mai Shari’a Edem Kufre ne ya umarci Secondus da kar ya sake bayyana kan sa a matsayin shugaban PDP biyo bayan ƙarar da wani ɗan jam’iyyar mai suna Enang Wani, ya shigar.

Kwana biyu bayan haka ne kuma wata kotu a Jihar Kebbi ta dawo da Secondus kan muƙamin nasa.

PDP ta bayyana sunan Elder Yemi Akinwonmi a matsayin shugaban riƙo, wanda shi ne mataimakin shugaba na yankin Kudu.