Home Labaru Hari: ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Mutane 4 A Katsina

Hari: ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Mutane 4 A Katsina

565
0

Wasu ‘yan ta’adda sun salwantar da rayukan wasu mutane hudu a garin Tsayu na karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

ASP Anas Gezawa,

 Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sanadan jihar ASP Anas Gezawa, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Anas Gezawa, ya ce bayan kisan ‘yan ta’addan sun kuma yi awon gaba da shanu hudu na al’ummar garin.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan ya ce kisan mutum hudun ya biyo bayan bin sawun ‘yan ta’adda har dokar daji ne da al’ummar garin suka yi domin daukar fansa.

Ganin wannan karfin hali da mutanen suka yi ya sa ‘yan ta’addan suka fusata wajen mayar da martani inda suka kai harin da ya salwantar da rayukan mutum hudu.

Anas Gezawa, ya nemi mazauna jihar da a koda yaushe su rika hadin gwiwa da hukumomin tsaro a yayin da suke yunkurin fatattakar miyagun mutane dake kai hare-hare a jihar.   y