Home Labaru Kasuwanci Badakala: Bankin Duniya Ya Tona Asirin Kamfanonin China

Badakala: Bankin Duniya Ya Tona Asirin Kamfanonin China

578
0

Babban Bankin Duniya ya tona sunayen wasu manyan kamfanonin gine-gine na kasar Sin wato China har guda shida, cewa an same su da laifin harkallar kwangiloli masu tarin yawa.

Bankin yace wadannan kamfanoni da ke gudanar da aiki a wurare daban-daban a Najeriya, sun karya ka’idojin ayyukan kwangilolin da bankin duniya ya gindaya a fadin duniya.

Kamfanonin da Bankin duniyan ya tona asirin su dai sun hada da China Railway Construction International Nigeria Company Limited, da China Railway 18th Bureau Nigeria Ltd,  da China Nageria Engineering Company Ltd, da  CCECC Nigeria Lekki Construction Ltd, da CCECC Railway Petroleum and Gas Company Ltd da kuma CCECC Nigeria Company Ltd.

A yanzu dai wadannan kamfanoni ne ke cin Karen su babu baka a wajen ayyukan kwangilolin gina hanyoyin jiragen kasa, da titinan gwamnatin tarayya da na jihohi, da gina rukunin gidaje na gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi, da gina tashoshin jiragen sama da ma harkokin man fetur a Najeriya.

Bankin Duniya ya ce ya haramtawa kamfanonin karbar duk wasu kwangiloli da suka shafi harkar kudaden da aka ranto daga Bankin, ko kwangilar bankin, har tsawon shekara daya, ammna sai suka cigaba  da gudanar da wasu kwangiloli ba tare da cikakken bayanin yadda aka kashe kudaden da hujjar abin da aka yi da kudaden ba.

Takardar nuna bacin rai da Bankin Duniya ya fitar a shafin sa na Intanet dai bai fayyace adadin kudaden da kamfanonin suka yi wa babakere ba.