Home Labaru Harae-Hare: Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutun 13 A Jihar Benuwe

Harae-Hare: Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutun 13 A Jihar Benuwe

237
0

Rahotanni daga jihar Benue sun ce ƴan bindiga sun kai hari wani ƙauye a jihar Benue inda suka kashe mutum 13 a wani rikici mai nasaba da rikicin masarauta.

Kafofin yaɗa labarai sun ambato rundunar ƴan sandan jihar da ta tabbatar da harin na cewa an kai harin ne ranar Litinin a ƙauyen Edikwu.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Benue Catherine Anene ta shaidawa Kamfanin dillacin laraban Faransa AFP cewa mutane da dama ne suka jikkata a harin yayin da kuma aka kone gidaje da dama.

Ta ce ƴan bindiga kusan 20 ne suka afkawa ƙauyen inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Kuma a cewarta jami’an ƴan sandan da aka tura sun gano gawawwaki 13.

Ƴan sandan kuma na zargin rikici kan masarauta ne ya haifar da harin, kuma ƴan sandan sun ce suna gudanar da