Home Labaru Har Yanzu Ba A San Adadin Daliban Kwalejin Yauri Da Su Ka...

Har Yanzu Ba A San Adadin Daliban Kwalejin Yauri Da Su Ka Rage A Hannun ‘Yan Bindiga Ba

56
0

Rahotanni daga jihar Kebbi na cewa, duk da an kubutar da wasu dalibai 30 da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su a kwalejin Yauri, har yanzu ba a iya tantance adadin daliban da su ka rage a hannun ‘yan bindigar ba.

Dalibai 30 da aka sace da wani malamin su dai sun kubuta daga hannun ‘yan bindigar ne bayan shafe tsawon watanni shida a hannun su.

Mai ba gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi shawara ta fuskar  yada labarai Yahaya Sarki ya tabbatar da cewa, an kubutar da daliban a wata sanarwa da ya fitar kamar yadda rahotanni su ka ruwaito.

Yahaya Sarki ya kara da cewa, za a duba lafiyar wadanda aka sako kafin a mika su ga iyalan su.

Al’ummomin yankin arewa maso yamma da tsakiyar Nijeriya dai na ci-gaba da zama cikin fargaba sakamakon hare-haren ‘yan bindigar da gwamnati ta ayyana a matsayin yan ta’adda.