Home Labaru Gwamna Wike Na Farautar Mutane 19 Da Ke Tace Danyen Mai Ba...

Gwamna Wike Na Farautar Mutane 19 Da Ke Tace Danyen Mai Ba Bisa Ka’Ida Ba

85
0

Gwamnan Nyesom Wike na jihar Rivers, ya bayyana neman wasu mutane 19 da ke gudanar da ayyukan tace danyen mai ba bisa ka’ida ba ruwa a jallo.

Nyesom Wike, dai ya ce ayyukan mutanen su na haddasa barna ga yanayi a jihar, lamarin da ya bayyana a matsayin babban laifi.

Gwamnan ya bayyana haka ne, a wani jawabin musamman da ya yi wa al’ummar jihar, inda ya umurci shugaban ma’aikatan jihar ya nemi daraktan ma’aikatar makamashi ta jihar Temple Amakiri, domin yin bayani a kan zargin tallafa wa ayyukan fasa bututtun mai ba bisa ka’ida ba.

Haka kuma ya yi umarnin a mika shi ga ‘yan sanda domin bincike tare da gurfanar da shi gaban kuliya kamar yadda gidan talabijan na Channels ya ruwaito.

Gwamnan, ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa, gwamnatin sa ta kudiri aniyar ganin ta shawo kan matsalar ta hanyar rugujewa, tare da rurrufe duk wasu wuraren da ake tace danyen mai ba bisa ka’ida ba a fadin jihar.