Home Labaru An Samu Bullar Nau’In Kwayar Cutar Shan-Inna A Wasu Jihohi

An Samu Bullar Nau’In Kwayar Cutar Shan-Inna A Wasu Jihohi

61
0

Wasu rahotanni na nuni da cewa, an samu rahoton bullar wata kwayar nau’in cuta dangin Shan-Inna a Jihohin Nijeriya 19.

Jihar Bauchi dai na daya daga cikin jihohin da nau’in cutar ya bulla a yankunan kananan hukumomi 12 na jihar.

Kananan hukumomin da aka gano kwayar cutar ta bulla sun hada da Toro da Warji da Darazoda Misau da Dambam da Zaki da Jama’are da Alkaleri da Ganjuwa da Bauchi da Katagum da kuma Shira.

Shugaban Hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar Bauchi Dr. Rilwan Mohammed, ya ce an dukufa wajen wayar da kan jama’a tare da hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, yayin da aka kaddamar da Allurar riga-kafi a kan iyakokin jihohi Makwafta.