Home Labaru Hangen Nesa: Osinbajo Ya Bayyana Hadin Kai A Matsayin Mafita Ga ‘Yan...

Hangen Nesa: Osinbajo Ya Bayyana Hadin Kai A Matsayin Mafita Ga ‘Yan Nijeriya

267
0
Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasa
Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasa

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, da jigon jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu, sun bayyana hadin kai tsakanin ‘yan Nijeriya a matsayin hanya mafi dacewa ta magance rashin tsaro da bambance-banbancen kabilanci da su ka addabi kasar nan.

Jiga-jigan na APC biyu sun bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da wani littafi yayin murnar cikar tsohon gwamnan jihar Ogun Cif Olusegun Ogbah shekaru 80 da haihuwa da ya gudana a Legas.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, jigon jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu

Yayin gudanar da taron, Osinbajo ya jaddada muhimmancin hadin kai domin yaye annobar kabilanci da ta mamaye zukatan ‘yan Nijeriya.

Osinbajo, ya kuma bayyana ta’addanci a matsayin wata muguwar masifa da ba ta bambamce tsakanin kabilu da addini ko kuma akidar siyasa ba.Ya ce dole ‘yan Nijeriya su hada kai wuri guda domin tabbatar da samun kyakkyawar makoma

Leave a Reply