Home Labaru Nade-Nade: Shugaba Buhari Ya Nada Farfesa Galadima A Matsayin Shugaban NIPSS

Nade-Nade: Shugaba Buhari Ya Nada Farfesa Galadima A Matsayin Shugaban NIPSS

259
0
BEBEJOfotography+2348067498331

 Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci majalisar dattawa ta amince da nadin Farfesa Habu Galadima a matsayin sabon babban daraktan cibiyar koyar da dabaru da tsare-tsaren mulki ta kasa da ke Kuru a jihar Filato.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan ya karanto wasikar da shugaba Buhari ya aika wa majalisar yayin zaman ta na ranar Talata nan.

Majalisar Dattawa

Buhari ya ce sashe na 8 (5) na dokokin hukumar ne ya ba shi ikon rubuta wasikar da ya aike wa majalisar a ranar 9 ga watan Yuli.

Shugaba Buhari, ya bukaci ‘yan majalisar su ba shi hadin kai wajen tabbatar da nadin Farfesa Galadima a matsayin shugaban Cibiyar ba tare da wata matsala ba.

Haka kuma, shugaba Buhari ya hada da takardun Farfesa Galadima da ke dauke da irin karatun da ya yi da gogewarsa a kan aiki da kuma duk wasu bayanai da za su taimaka wa majalisar wajen tantance shi.

Leave a Reply