Home Labaru Bajinta: Kasar Amurka Za Ta Karrama Sowore Da Kambin Girmamawa

Bajinta: Kasar Amurka Za Ta Karrama Sowore Da Kambin Girmamawa

376
0
Bajinta: Kasar Amurka Za Ta Karrama Sowore Da Kambin Girmamawa
Bajinta: Kasar Amurka Za Ta Karrama Sowore Da Kambin Girmamawa

Mawallafin jaridar Sahara Reporters, kuma shugaban gangamin juyin-juya-hali Omoyele Sowore, Kasar Amurka za ta karrama shi a matsayin fursunan Amurka na shekara ta 2019.

Hakan dai ya biyo bayan tsare shi na tsawon lokaci da hukumar jami’an tsaro ta farin kaya ta yi na tsawon lokaci, sannan ta kara kama shi bayan kotu ta bada umarnin sakin sa.

Rahotanni sun ce za a ba Sowore Kambin yabon ne daga hukumar kare hakkin dan Adam ta Tom Lantos da ke majalisar wakilai ta kasar Amurka.

An dai saki Sowore ne, bayan ministan shari’a Abubakar Malami ya bada umurni, lamarin da ya janyo wa ministan yabo da jinjina a fadin Nijeriya saboda jajircewar sa ta gyaran kasa.