Shugaban sashin jigilar jiragen sama na hukumar kula da Mahajjatan Najeriya, Mohammed Goni, ya ce Alhazan Najeriya za su fara dawo wa gida daga ranar Asabar 17, ga watan Agusta.
Muhammad Goni, ya bayyana hakan ne a wajen wani takaitaccen taro da aka gudanar da masu ruwa da tsaki inda ya ce jirgin farko, na Flynas-Airline zai baro kasa mai tsarki a ranar 17 ga wata zai da Mahajjatan Najeriya zuwa jihar Legas.
Ya kara da cewa bisa tsarin jigilar A da Flynas Airline ta bayar, jirage hudu na farko za su dauko Mahajjatan Legas ne, sannan na biyar zai kwaso na jihar Kebbi.
Ya shawarci Mahajjatan su takaita dauko jakunkunan hannu saboda kiyaye dokokin kamfanonin jigilar na kayyade adadin kayan da jirgi zai iya dauka.
Ana sa ran kamfanonin jiragen sama biyu da za su yi jigilar Alhazan za su kasance cikin shiri a tashar jiragen sama na Sarki Abdulaziz, da ke Jeddah a ranar 16 ga watan Augusta domin fara shirin dawo alhazan Najeriya gida.
You must log in to post a comment.