Home Labaru Kanu Nwankwo Ya Zama Mai Ba Gwamna Shawara

Kanu Nwankwo Ya Zama Mai Ba Gwamna Shawara

687
0

Tsohon dan wasan Najeriya da ya taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke kasar Ingila, Kanu Nwankwo, ya samu mukamin babban mai bawa gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, shawara a kan harkokin wasanni.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin Izuchukwu Akwarandu, sabon mai taimakawa gwamna a bangaren yada labarai.

Sanarwar ta bayyana cewa; gwamnan, ya karbi bakuncin daya daga cikin jaruman yan wasan kwallon kafa na kasa, Kanu Nwankwo, a gidan gwamnatin jihar Imo da ke Owerri, a ranar 14 ga watan Agusta, 2019.Papilo, kamar yadda masoyan sa ke kiran sa, ya gabatar da kyautar dan wasan kwallon kafa na nahiyar Afrika da ya lashe, wacce kuma aka bashi bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Afrika a kasar Misra inda ya ba gwamna kyautar wata rigar wasa ta musamman.

Leave a Reply