Home Labaru Hadin Kai: Yadda Gwamnonin Arewa Su Ka Kudiri Kawo Karshen Ta’addanci

Hadin Kai: Yadda Gwamnonin Arewa Su Ka Kudiri Kawo Karshen Ta’addanci

388
0

Gwamnonin jihohi 19 na yankin Arewacin Nijeriya, sun daura damarar neman kwararrun masana harkar tsaro domin shimfida tafarki da dabarun kawo karshen kalubalen rashin tsaro da ya yi wa yankin dabaibayi.

Haka kuma, gwamnonin su na neman samar da hanyoyin jituwa a tsakanin tanadin dokoki a Nijeriya, domin tabbatar da cewa duk masu barazana ga zaman lafiya doka ta yi aiki a kan su.

Kungiyar gwamnonin ta yanke wannan muhimmiyar shawara ne, yayin zaman da ta gudanar a Kaduna ranar Juma’ar da ta gabata, inda ta kafa wani sabon kwamiti, domin shimfida tafarki da dabarun tsarkake yankin Arewa daga ta’adar masu tada zaune tsaye.

Kwamitin, a karkashin jagorancin gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, zai samar da muhimman tsare-tsare da tubalin warware matsalolin rashin tsaro da su ka yi wa yankin Arewa dabaibayi.

Kungiyar gwamnonin, za ta kuma nemi ganawa da shugaba kasa Muhammadu Buhari, domin shigar da bukatu dangane da halin rashin tsaro da al’ummomin yankin Arewa ke fuskanta a yanzu.

Leave a Reply