Kungiyoyin kwadago da na fararen hula, sun shawarci gwamnatin Nijeriya ta jinkirta mika wa gwamnatocin jihohi cikon kudin Paris Club da yawan su ya kai Naira biliyan dari 649 har zuwa lokacin da za a rantsar da sabbin gwamnatoci a ranar 29 ga watan Mayu.
Kiraye-kirayen kungiyoyin dai na zuwa ne, bayan wata sanarwar ministar kudi da ke cewa gwamnati na gab da mika wa jihohin cikon kudaden, wanda shi ne kaso na karshe da ake maida masu tsawon lokaci.
Kungiyar kwadago ta kasa ta ce, kamata ya yi gwamnati ta jira zuwa kafuwar sabbin gwamnatoci a matakan jihohi don ganin kudaden sun amfani al’umma.
Idan dai za a iya tunawa, a shekarar da ta gabata, akwai zarge-zarge da su ka dabaibaye yadda gwamnaonin su ka kashe wani kaso na kudin, wanda tun farko shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci su yi amfani da su wajen biyan hakkokin ma’aikata.
You must log in to post a comment.