Home Labaru Kasuwanci Tattalin Arziki: Dole Nijeriya Ta Dage Yin Ajiya A Asusun Tara Rarar...

Tattalin Arziki: Dole Nijeriya Ta Dage Yin Ajiya A Asusun Tara Rarar Ribar Danyen Mai Ministar Kudi

744
0

Ministar kudi ta Nijeriya Zainab Ahmed, ta ce ya zama dole gwamnati ta jajirce wajen maida hankali ta na tara rarar ribar danyen mai a cikin Asusun Hukumar Tanadin Kudaden Zuba Jari ta kasa.

Ta ce hakan ya zama wajibi, domin samun damar ci-gaban inganta asusun, ganin yadda a karo na shida kenan cikin shekaru biyar da kafa shi ana sanar da irin ribar da ake samu.

Ministar ta bayyana haka ne, yayin wata ganawa da manema labarai kamar yadda ta saba shiryawa duk bayan watanni uku, domin sanar da ci-gaba da kuma halin da Ma’aikatar kudi ke ciki.

Ta ce gwamnati na aiki don ganin Majalisar Bada Shawara a kan Tattalin Arziki, ta tabbatar da cewa ta na tanadin kudaden Rarar Ribar Danyen Mai don karfafa hukumar da kudaden da ake tarawa.

Ministar ta kara da cewa, hakikanin gaskiya hukumar ta na matukar kokarin ganin ta na ririta Asusun Tsimi, wanda ke hana gwamnatoci tagayyara a ranar da aka samu akasin rashin wadatar kudaden shiga.

Leave a Reply